Sports
Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Coutinho, Haaland, Traore, Puig, Wirtz, Di Maria
Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Aston Villa na da zaɓin saye ɗan wasan Brazil da ya tafi zaman aro Philippe Coutinho, sai dai Arsenal na sayon ta saye shi daga Barcelona a wannan kakar idan bai koma hannun Steven Gerrard ba baki daya. (Sport – in Spanish)
Abin da Erling Braut Haaland ya fi bai wa fifiko a yanzu shi ne komawa kungiyoyin Sifaniya wato Real Madrid ko Barcelona, duk da cewa a wannan makon an yi ta samun rahotanni da ke danganta ɗan wasan na Borussia Dortmund mai shekara 21 da Manchester City. (Sport)
Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce ƙungiyar ba zai kulla kwantiragi ba kan Haaland a wannan kakar muddin yarjejeniya na iya jefa ƙungiyar cikin matsalar kudi. (TV3, via Goal)
Barcelona ta matsu ta dauko dan wasan gefe Adama Traore mai shekara 26 daga Wolves a wannan kakar, ta na kuma iya mika tayi kan Riqui Puig mai shekara 22. (90Min)
Ƙungiyoyin Manchester United, Liverpool da Newcastle na farautar ɗan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz, sai dai ɗan wasan mai shekara 18 da ke buga tsakiya ya samu mumunan raunin da ka iya zaunar da shi har karshen kaka babu wasa. (Express)
Dan wasan Argentina Angel di Maria ya yanke hukuncin barin Paris St-Germain a wannan kakar kuma yana iya komawa Benfica. (AS – in Spanish)
Koci Mauricio Pochettino da ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe na shirin jagorantar gagarumin shirin bakwana da Paris St-Germain a wannan kakar. (L’Equipe, via Mirror)
Zinedine Zidane mai yiwuwa ya maye gurbin Pochettino a PSG, yayinda shi kuma ke harin Real Madrid. (El Nacional – in Catalan)
Arturo Vidal ya shirya bankwana da Inter Milan kuma tuni Flamengo ta nuna zawarcinta kan ɗan wasan na Chile mai shekara 34. (Calciomercato – in Italian)
Roma na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Barcelona Sergino Dest, mai shekara 21. (Corriere dello Sport – in Italian)
