Daga Usman Abdullahi jibirin
Rahotanni sun ce shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yana umartar a ɗanɗana abincinsa kafin ya ci.
Putin ya maye gurbin dukkan ma’aikatansa 1,000 a watan da ya gabata.
Putin, wanda tsohon ɗan leken asiri ne, yana tsoron kada a saka masa guba.
A Rasha a kan sanya guba ga mutanen da ake son kashewa.
A baya an taba saka wa jagoran ‘yan adawar Rasha guba, duk da cewa ya samu ya tsira da ransa
