Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mount, Terrier, Neves, Laporte, Zinchenko, Aguerd

Published

on

Daga Maryam bashir musa 

 

 

 

Manchester United na duba yiwuwar raba Mason Mount, dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila mai shekara 23 da Chelsea. Har yanzu dan wasan bai sanya hannu kan sabuwar kwantiragi a Stamford Bridge ba (Sun)

Liverpool na ci gaba da sa ido kan Martin Terrier, dan wasan gaba mai shekara 25 na Rennes da kasar Faransa a matsayin wanda zai maye gurbin Sadio Mane, wanda ake sa ran zai bar kungiyar. (Mirror)

Advertisement

Kocin Barcelona Xavi ya tattauna da Ruben Neves, dan wasan kungiyar Wolves da Portugal mai shekara 25 kan kokarin saye shi. (Sport – in Spanish)

Har yanzu Juventus na son sayen Aymeric Laporte, dan wasan baya na Sfaniya da Manchester Citymai shekara 28. (Corriere dello Sport via Manchester Evening News)

West Ham daf da sayo Nayef Aguerd, dan wasan baya na Rennes. (Evening Standard)

Arsenal na ci gaba da nuna sha’awar dauko Youri Tielemans dan wasan tsakiya na Leicester mai shekara 25. (Fabrizio Romano)

Chelsea ta sake bayyana sha’awarta kan raba Sergiono Dest, dan wasan bayan na Barcelona mai shekara 21. (Mail)

Dan wasan gaba na Paraguay mai shekara 28, Miguel Almiron ba zai bar Newcastle United ba a karshen kakar wasa ta bana. (Chronicle Live)

Advertisement

Inter Milan na tattaunawa da lauyoyin Romelu Lukaku, dan wasan gaba na Chelsea mai shekara 29, domin duba yadda za a mayar da shi gasar Serie A. (Guardian)

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending