Connect with us

Sports

Dawowar Messi zuwa Barcelona ba abu ne mai yiwuwa ba yanzu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Xavi Hernandez, a yau Talata ya ce dawowar Lionel Messi zuwa ƙungiyar ba abu ne da zai yi wu ba a halin yanzu, sai dai kuma bai fidda ranar za su sake haɗuwa a kwallon kafa ba nan gaba.

Gwamnatin Kano ta gano ma’ajiyar gurɓataccen taki da ake sayar wa da manoma

Advertisement

Tsohon dan wasan na Barca duk da haka ya yi watsi da kwatanta shi da ake tsakaninsa da manyan kociyoyin ƙungiyar guda biyu.

Shekaru 21 da Messi ya yi tare da FC Barcelona sun ƙare a watan Agustan da ya gabata lokacin da ya koma Paris Saint-Germain, PSG, kyauta duk da Barca na fama da matsalar tattalin arziki.

Advertisement

Duk da haka, kwallaye shida da ya ci a gasar League One a shekarar sa ta farko a Paris, inda hakan shine karo na biyu da bai yi kokari ba tun bayan shekara 18 a 2005/2006.

Tsohon abokin wasan Messi kuma kocin FC Barcelona na yanzu Xavi, ya shaida wa taron manema labarai cewa irin wannan matakin ba zai yuwu ba, aƙalla a yanzu.

Advertisement

“Yana da kwantiragi da PSG kuma ba zai yiwu ba a yanzu,” in ji Xavi, inda ya ce shi yanzu wasan sada zumuntar Barca da Juventus a Dallas ranar Talata me a gaban sa.

“Messi shine gwarzon dan kwallon kafa a duniya da kuma a tarihi. Shugaba Laporta ya riga ya ce labarin Messi da Barca bai kare ba, amma yanzu ba lokaci ne da za a yi magana akai ba. “

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending