Connect with us

News

2023: Atiku ya naɗa Shekarau, Saraki, Anyim da wasu a matsayin mashawartan yaƙin zaɓensa

Published

on

Atiku

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi wasu muhimman naɗe-naɗen mukamai na masu ba shi shawara na musamman da nufin karfafa tawagar yakin neman zabensa na shugaban kasa.

Advertisement

Hakan na zuwa ne gabanin fara yakin neman zaben 2023 a ranar Laraba.

Wata sanarwa da Paul Ibe, mai baiwa Atiku Abubakar shawara kan harkokin yada labarai ya fitar, ta ce waɗanda aka nada sun hada da tsoffin shugabannin majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki a matsayin manzo na musamman ga dan takarar shugaban kasa da kuma Sanata Pius Anyim, a matsayin mai ba da shawara na musamman.

Advertisement

“Haka zalika sauran waɗanda a ka nada a matsayin mashawarta na musamman ga dan takarar akwai tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da Sanata Ehigie Uzamere,” inji sanarwar.

A cewar sanarwar, an kuma nada tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus a matsayin mai baiwa dan takarar shugaban kasa shawara a fannin fasaha.

Advertisement

Sanarwar ta cenadin zai fara aiki nan take.

“Atiku Abubakar ya bukaci wadanda aka nada su yi amfani da dimbin gogewar da suka samu na siyasa wajen ganin cewa yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya samu gagarumar nasara a zaben 2023.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending