News
NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare Ta 2022
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar da ke Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandare da aka yi a watan Yulin 2022 a fadin Najeriya.
Shugaban hukumar, Farfesa Danladi Wushishi ne bayyana hakan a Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Alhamis.
Zaben 2023: ‘yan takara sun sa hannu a kan zaman lafiya
A cewarsa, daga cikin dalibai 1,209,703, da suka zauna jarabawar a bana, kaso 60.74, wato dalibai 727,864 ne suka samu akalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
Ya ce idan aka kwatanta da sakamakon 2021 inda dalibai 878,925 (kaso 71.64 cikin 100) da suka samu turancin da Laissafi, a bana an sami raguwar kaso 10.9 ke nan.
Muna tafe da karin bayani…
