News
Ebola ta sake hallaka ma’aikacin lafiya a Uganda
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Ma’aikatar lafiya ta Uganda ta tabbatar da mutuwar wata ma’akaciyar lafiya, wadda ke aikin allurar hana radadin ciwo yayin da za a yi wa mutum tiyata.
Sanarwar da Ministar Lafiya Jane Ruth Aceng ta fitar ta ce, Margaret Nabisubi, mai shekara 58, ta rasu ne cikin daren da ya gabata, wayewar garin Larabar nan.
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Kori Manyan Jami’ai 7, Ta Rage Matsayin Wasu 10
Wasu ma’aikatan lafiya sun samu kansu cikin hadarin kamuwa da kwayar cutar lokacin da suka yi wa mutum na farko da ya kamu da cutar, wanda za a yi masa tiyata, daga nan ne aka kwantar da su a asibitin yanki na Fort Portal.
Wani dalibi dan kasar Tanzania da ke koyon aikin likita, wanda na daga cikin ma’aikatan shi ma ya rasu a karshen mako.
Haka shi ma wani karamin ma’aikacin lafiya a gundumar Kagadi wanda ba ya cikin wancan ayarin shi ma cutar ta hallaka shi.
Sannan ana zargin cutar ta Ebola kuma ta kashe wata ungozoma duk a cikin ‘yan kwanakin nan a kasar ta Uganda.
Ma’aikatan lafiya na korafin rashin isassun kayan aiki na kariya a farkon kwanakin barkewar cutar.
Alkaluman da hukuma ta fitar sun nuna cewa mutum 43 ne suka kamu da cutar tun bayan da ta barke mako biyu da ya gabata kuma 10 daga cikinsu sun mutu.
Jami’an lafiya sun ce sun gano sama da mutum 800 da ake zargin sun yi mu’amulla da wadanda kwayar cutar ta harba.
BBC NEWS
