Connect with us

News

Yobe: Mutane 6,592 Sun Rasa Matsugunansu Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN 

 

 

 

 

Dr. Mohammed Goje, Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), ya ce ambaliyar ruwa da guguwar iska ta kashe mutane 75 a cikin al’ummomi 255 a cikin watanni shida da suka gabata.

Advertisement

Goje ya bayyana haka ne ga manema labarai a Damaturu lokacin da yake magana kan irin barnar da iftila’in ya janyo a kananan hukumomi 17 na jihar.

Yanzu-Yanzu: Gobara ta Tashi a Kusa Da Gidan Rediyon Nasara a Kano

Ya kara da cewa, ambaliyar ta kuma kwashe manyan tituna guda 10 tare da raba mutane 6,592 da muhallansu a wasu yankunan Bade, Karasuwa, Jakusko, Gujba, da Gulani.

A cewar Goje, mutane 75 da aka ruwaito sun mutu sun kasance sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da iska tare da wasu karin rayukan mutane da ke cikin hadari a fadin kananan hukumomi 10 kuma sama da 200 sun samu raunuka daban-daban kuma an yi musu magani kyauta.

Sakataren zartaswar, ya koka da cewa, a yawancin al’ummomin da abin ya shafa, musamman Gulani, Gujba, Tarmuwa, da Jakusko inda aka katse hanyoyin shiga, isar da tallafin ceton rai ya kan yi wahala.

Ya ce SEMA tare da sauran ma’aikatu da hukumomi da kuma masu aikin sa kai na cikin gida suna aiki ba dare ba rana don taimakawa al’ummomin da abin ya shafa kamar yadda Gwamnan Jihar ya umarta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending