Connect with us

News

An Kama Fasto Mai Garkuwa Da Mutane

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Dubun wani fasto da ke garkuwa da mutane ta cika a Jihar Adamawa.

 

Advertisement

Kotun Majistare ta jihar ta sa a tsare faston a gidan yari bayan ya amsa tuhumar da ake masa na yunkurin garkuwa da wani magidanci.

Hukumar Kwastam ta kama Shinkafa da kudinta ya kai N200m a Bauchi

Advertisement

Fasto Joel Saul ya amsa laifin ne bayan dan sanda mai gabatar da kara, ASP Ezra Bulus, ya karanta masa tuhumar da ake masa na yunkurin yin garkuwa da mutane a gaban Alkali Alheri Ishaku.

 

Advertisement

ASP Ezra Bulus ya shaida wa kotun cewa Fasto Joel ya yi yunkurin yin garkuwa da wani magidanci a kauyen Mangere da ke kan hanyar Numan saboda mutumin ya ki ba shi Naira miliyan daya.

 

Advertisement

ASP Ezra ya ce bayan malamin addinin ya nemi mutumin ya ba shi kudin ko kuma a yi garkuwa da shi ko iyalansa ne ya aika wasikar barazanar sace mutumin har gida.

Ya kuma yi wa mutumin barazanar cewa kada ya kuskura ya bar gidansa sannan ya rika kira ya ji ko an biya kudin fansar.

Advertisement

 

Daga baya jami’an tsaro suka bibiyi lambar da ya yi amfani da ita wajen kiran mutumin har aka gano shi.

Advertisement

 

Bayan wanda ake zargin ya amsa laifin, ASP Ezra ya bukaci kotun ta dage shari’ar don ’yan sanda su samu ji daga Sashen Gabatar da Kara na Gwamnatin Jihar Adamawa.

Advertisement

 

Daga nan alkalin ya amince da hakan sanna ya ba da umarnin tsare faston a gidan yari.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending