News
Ana neman ɗan a-daidaita-sahun da ya ɗauko kurar da ta kuɓuce a Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar kula da sufurin ababen-hawa a jihar Kano (KAROTA) ta ce ta na ci gaba da neman wani mai baburin a-daidaita-sahu ruwa a jallo bayan ya ɗauko wata kura da ta yi ƙoƙarin tserewa a tsakiyar kasuwa.
Hukumar ta ce jami’anta suna neman mai a-daidaita-sahun saboda abin da ya yi ya saɓa wa doka, don kuwa bai kamata ya ɗauko dabbar daji a cikin babur ba.
Benzema Ya Lashe Kyautar Ballon D’or Na Farko
Mai magana da yawun hukumar, Nabulisi Abubakar ya shaida wa BBC cewa kura ba tunkiya ko akuya ba ce, dabba ce mai hatsari da bai kamata a bar ta tana gararamba a cikin mutane ba.
“Muna ci gaba da neman ɗan a-daidaita-sahun a yanzu haka, kuma muna da lambobin babura guda biyu da muke zargi, matuƙar kuma muka kama direban, to kotu za mu kai shi kai tsaye
Daily Nigeria Haus
