Connect with us

News

Kwankwaso Zai Kawo Sama Da Kuri’a Miliyan 50 Arewa A Cewar Buba Galadima.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Tsohon mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar APC, Injiniya Buba Galadima, ya ce Kwankwaso ne zai lashe zabe a dukkan jihohin arewa 19 a zaben shugabancin kasa na 2023 dake zuwa.

Advertisement

Cikin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV, a jiya Alhamis, buna Galadima yace Kwankwaso zai lashe zabe a shiyoyi uku na arewa kuma ya samu kuri’u a inda abokan hamayyarsa ke da karfi.

PDP bata kan takardar kada kuri’a saboda karfin ta a kudu maso gabas ne wanda kuma Peter Obi suke yi.

Advertisement

Dan Takarar Gwamnan Jihar ADP ya baiwa kungiyar likitocin Najeriya tabbacin mayar da Kano cibiyar yawon bude ido ta lafiya a nahiyar Afirka.

Wurin da PDP ke da karfi kuma shi ne kudu maso kudu. Kamar yadda Wike baya goyon bayan Atiku, kudu maso kudu ta kubuce masa.”

Advertisement

Buba Galadima yace Arewa dukkanta ta Kwankwaso ce saboda zai kawo Taraba, Adamawa, Gombe da Bauchi wanda ya hada da gwamnoninsu.

“Zai yi nasara a arewa maso gabas, arewa ta tsakiya kuma ya kawo arewa maso yamma. Idan aka hada duka, zasu samu kuri’u sama da miliyan hamsin.

Advertisement

Kwankwaso zai samu wani kaso a kudu maso kudu, kudu maso gabas da kudu maso yamma.

Saboda haka inada tabbacin kada da daɗa, kada ka rage Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa a cewar Buba Galadima.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending