Connect with us

News

Dan sanda ya kashe abokin aikinsa da almakashi a Kebbi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi a Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike kan mutuwar wani jami’inta ASP Shu’aibu Sani Malumfashi, bayan wani faɗa da takwaransa mai muƙamin ASP.

 

Advertisement

Rundunar ta ce, a ranar 19 ga watan Oktoban 2022, ne da rana jami’anta biyu da ke aiki a ofishinsu da ke Argungu wato ASP Abdullahi Garba, da kuma ASP Shu’aibu Sani Malumfashi, suka samu sabani kuma a dalilin haka ne suka kaure da fada.

Kwankwaso Zai Kawo Sama Da Kuri’a Miliyan 50 Arewa A Cewar Buba Galadima.

Advertisement

Rundunar ta bakin jami’in hulda da jama’arta SP Nafi’u Abubakar, ta shaida wa BBC cewa, bayan jami’na ‘yan sandan sun kaure da fada ne sai ASP Abdullahi Garba, ya yi amfani da almakashi ya soki abokin aikin nasa a hakarkari.

 

Advertisement

SP Nafi’u Abubakar, ya ce bayan soka masa almakashin ne sai ya yanke jiki ya fadi kasa, anan ne DPO din da ke ofishin ya garzaya ya je wajen ya taradda abokin aikin nasu a kwance cikin jini anan ne aka kwashe shi aka kai asibiti.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan a Kebbi, ya ce ” Bayan samun labarin abin da ya faru a tsakanin jami’an namu gashi kuma har da rasa rai, mun kadu gaskiya, saboda ba dadi mutum ya bar gida ya tafi aiki lafiya lau amma kuma daga baya akai wa iyalansa gawarsa ace gashi ya mutu sakamakon sabani da ya samu da abokin aikinsa.”

Advertisement

 

Ya ce, hankalin iyalansa ya yi matukar tashi tun da mutum ne mai iyali.

Advertisement

 

SP Nafi’u Abubakar, ya ce bayan afkuwar wannan lamari a yanzu an kai wannan batu zuwa babban ofishinsu na binciken manyan laifuka da ke Birnin Kebbi wato CID, don a gudanar da bincike a kan ainihin abin da ya faru a tsakanin jami’an nasu da har suka kaure da fada aka kuma samu asarar rai.

Advertisement

 

Ya ce,” Wanda ake zargin wato ASP Abdullahi Garba, na nan a tsare a yanzu haka har sai an kammala bincike kafin daga bisani kuma a kai shi kotu.”

Advertisement

 

Jami’in hulda da jama’ar ya ce, sakamakon afkuwar wanann iftla’i a yanzu kwamshinan ‘yan sandan jihar ta Kebbi ya gargadi jami’na ‘yan sandan da ke aiki a jihar da su zauna lafiya da junansu.

Advertisement

 

Sannan kuma na shawarce su da idan har wani daga cikinsu ya yi wa wani ba daidai ba, to akwai in da za su iya kai wa kara a cikin ofisoshinsu ba sai sun dauki doka da hannunsu ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending