News
Gangar ɗanyen mai dubu 700 a ke sace wa kullum a Nijeriya – Minista
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Najeriya na asarar a kalla gangar danyen mai dubu 700 ga barayi kulli-yaumin, in ji karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva.
Ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye daliban Cibiyar Harkokin Man Fetur, PTI na 2002 a jiya Asabar a Effurun, Delta.
Harin bom yayi sanadiyyar mutuwar mutum 100 ALSHA,BAB
Ministan, wanda ya samu wakilcin Gabriel Aduda, babban sakatare a ma’aikatar albarkatun man fetur, ya ce gwamnatin tarayya na yin haɗin gwiwa domin daƙile wannan matsalar.
Ya ce satar danyen mai ta yi illa sosai ga harkar canjin kudaden ƙasar waje a Nijeriya.
“Ƙasar nan na asarar gangar danyen mai kusan 700,000 a kowace rana sakamakon sace wa da a ke yi. Mummunan illar hakan shi ne raguwar samar da danyen mai da raguwar kudaden shiga na kasa,” inji shi.
Ya ce ma’aikatar man fetur za ta hada kai da majalisar dokokin kasar don tabbatar da cewa an ba da cikakkiyar kulawa da karfafa wa ga gyaran dokar mai ta PTI.
