Connect with us

News

Harin bom yayi sanadiyyar mutuwar mutum 100 ALSHA,BAB

Published

on

Somalia

DAGA  YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya tabbatar da cewa aƙalla mutum 100 ne aka kashe sakamakon wasu hare-haren ƙunar baƙin wake biyu da aka kai da motoci a wajen ma’aikatar ilimi ta ƙasar. An kai harin ne a jiya Asabar a Mogadishu babban birnin ƙasar.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa akwai aƙalla mutum 300 da suka samu raunuka sakamakon wannan harin.

Advertisement

BBC Hausa ta rawai to Mista Mahmud ya kai ziyara wurin da aka kai harin inda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana cewa cikin mintoci kaɗan motocin suka ƙaddamar da hare-haren.

Shaidu sun bayyana cewa ita motar ta biyun ma ta kai harin ne a yayin da jama’a suka garzayo da kuma motar ɗaukar marasa lafiya domin kai agaji.

Advertisement

Babu wata ƙunigiya da ta ɗauki nauyin kai harin zuwa yanzu amma ƙungiyar al-Shabab da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta sha ƙaddamar da irin waɗannan hare-hare.

Ƙungiyar ta al-Shabab ta yi sanadin mutuwar dubban mutane da dama  a ƙasar ta Somalia da kuma rabba miliyoyi mutane daga gudajen su

Advertisement

A ƴan kwanakin nan gwamnatin ƙasar ta rinƙa zafafa hare-hare kan ƴan ƙungiyar, lamarin da ya jawo ita ma ƙungiyar ke zafafa hare-hare.

Ko a kwanakin baya sai da ƙungiyar ta kai hari a wani otel inda ta kashe mutane da dama

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending