News
Zamu kaddamar da sabon asibitin da kaf arewa babu kamar sa~Tambuwal
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jahar sokkoto alhaji aminu waziri tambuwal yace, gwamnatin sa ta kusa kaddamar da sabon asibitin da kaf yankin arewa maso gabas babu irin sa.
Gwamnan ya bayyana hakanne a Wata tattaunawar sa da sashin Hausa na muryar amurka (VOA)
Kotu ta yanke wa shugaban hukumar EFCC hukunci bisa laifin cin zarafi kotu
Yana mai cewa Kashi 75 cikin 100 na aikin ya kammala kuma aikin ana saran zai kawo sauye sauyen abubuwa da babu wata gwamnatin data taba kawo irin sa akaf jahar ta sokkoto dama yankin arewa maso gabashin nigeria. Inji shi
Tambuwal yakarada cewa Zamu kawo kayan aiki daga kasashen waje domin bunkasa harkar lifiya a fadin jahar ta Sakkwato
Yace gwamnatin sa zata daibi sabbin ma,aikatan lafiya da saka na,urori masu kwakwalwa da CCTV camera domin bunkasa harkar lafiya a jahar
Yana mai cewa Gwamnatin mu ta bawa fannin lafiya mahimmanci sosai Kuma zamuyi iya kokarin mu wajen ciyar da jahar mu gaba cewar gwamna tambuwal
