Connect with us

News

Da Ni Za Ayi Gwagwarmayar Kamfen Din Tinubu Har Sai Mun Kai Ga Nasara – Buhar

Published

on

Buhari da tinubu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin ganin dan takarar shugaban Kasa na APC, Bola Tinubu ya kai ga nasara a zaben dake tafe.

Advertisement

Buhari ya bayyana haka a wajen taron Kamfen din jam’iyyar APC da aka yi a garin Jos, Jihar Filato,

El-Rufa’i Ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Ta Gaggauta Cire Tallafin Man Fetur.

Advertisement

 

Shugaba Buhari ya bayyana wa magoya bayan jam’iyyar APC cewa bai zo garin Jos don ya karanta doguwar jawabi bane,

Advertisement

”Na zo ne domin in mika tutar APC ga dantakarar shugaban kasan mu, wanda zai gaje ni, wato Bola Tinubu.

”Jam’iyyar mu ta dauki matsaya kuma matsayar ita ce, Tinubu, saboda haka dukkan mu za mu dunkule mu yi aiki tukuru don ganin Tinubu da jam’iyyar APC sun kai ga nasara.

Advertisement

Wannan tafiya ta mu ce duka kuma babu gudu ba ja da bawa, nasara ce kawai a gaban mu kuma ita muke bida.

A nasa jawabin dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Tinubu, ya ce zai dora kan nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Advertisement

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana cewa Buhari ya taka rawar gani a fannin samar da ababen more rayuwa tare da kafa ginshikin bunkasa noma da sauran fannoni.

“Ba mu da kwanciyar hankali, sai mu ka koma ga Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya kuma fara farfadowa da kwato Najeriya.

Advertisement

“Ya fara ne da lalata tutocin ƴan ta’adda abisa tsari, dabara da kuma hikima, kuma a yau babu wata tuta a kananan hukumominmu a Nijeriya.

“Najeriya ta fara nutsewa amma sai Buhari ya tsamo mu ya kuma ce Najeriya ba za ta nutse ba a zamaninsa da kuma lokacin APC,” inji shi.

Advertisement

Ya bayyana cewa Buhari ne ya jagoranci gudanar da zaben fidda-gwani na gaskiya da inganci wanda ya samar da shi a matsayin mai rike da tuta.

Shima dai a nasa jawabin, A jawabin sa, shugaban APC ta kasa, Sanata Adamu Abdullahi ya shaida cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zarce alkawuran da ya dauka a lokacin da yaki neman takarar shugaban cin Najeria.

Advertisement

”Duka alkawuran da Buhari ya dauka ya cika su cif-cif har ya zar ce yadda ake tsammani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending