News
Kasar rasha tace babu Wani harin ta,addanci da takai Poland
DAGA KABIRUBASIRU FULATAN
Rahotanni na cewa wasu makaman Rasha sun faɗa ƙasar Poland inda suka yi sanadiyyar rayukan mutum biyu da ke aiki a gona.
Bayanan sun ce makaman sun faɗa ne a wani yankin Poland da ke dab da kan iyakarta da Ukraine.
2023: Zan ɗora a kan nasarorin Buhari — Tinubu
Idan har bayanan suka zama gaskiya, zai zama karon farko da makaman Rasha suka faɗa cikin wata ƙasa da ke da wakilci a ƙungiyar NATO tun bayan ɓarkewar faɗa tsakanin Rasha da Ukraine.
BBC Hausa ta rawai to Sai dai ma’aikatar tsaro ta Rasha ta ce babu wani hari da aka kai kamn iyakar Poland da Ukraine.
A wata sanarwa da ta fitar, Rasha ta bayyana rahotannin a matsayin wani mataki na ingiza wutar rikicin da ke gudana.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka ya nanata cewa ƙasarsa za ta kare duk wani yanki na ƙasashe NATO
