Connect with us

News

Ta Tabbata An Sallami Shugaban Hukumar NYSC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Ministan Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare, ya tabbatar da sallamar Darakta-Janar na Hukumar Kula da Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), Birgediya-Janar Mohammed Fadah.

Advertisement

 

A safiyar Juma’a ne ministan ya tabbatar mana da sallamar, wadda tun kafin wayewar gari kafofin sada zumunta suke ta yadawa.

Advertisement

 

Gwamnatin Najeriya ta tsaurara matakan tsaro a ofisohin INEC da ke faɗin ƙasar

A amsarsa ga sakon da wakilinnmu ya tura masa na neman sanin hakikanin labarin, Ministan ta ce, “gaskiya ne,” an sallami shugaban na NYSC.

Advertisement

 

Aminiya ta samu rahoto cewa an umarci Birgediya-Janar Mohammed Fadah ya mika duk kayayyakin Hukumar NYSC da ke hannunsa ga jami’in da ke biye da shi a matsayi, wanda shi ne zai kasance Mukaddashin Darakta-Janar na hukumar.

Advertisement

 

Tun da farko wata majiya a Fadar Shugaban Kasa ta tsegumta wa wakilinmu cewa shugaban na NYSC na dab da rasa kujerarsa, bayan ministan ya nuna rashin gamsuwa da kamun ludayinsa.

Advertisement

 

Majiyar ta ce, “Abin ya kai ga ministan ya kai korafi game da dabi’un wasu manyan mutane; Na sa ba wannan ne na karshe ba.”

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending