Connect with us

News

Ogun : kotu ta Sanya ranar yanke hukunci kan halattaccen Dan takarar gwamna na jam,iyyar PDP

Published

on

Jahar Ogun

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya sanya ranar 1 ga watan Disamba, 2022 domin yanke hukunci kan tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Ogun a zaben shekarar 2023.

Advertisement

 

Mai shari’a Ekwo ya tsayar da ranar ne bayan ya yi muhawara da jam’iyyun.

Advertisement

 

Yan sanda sun gano gida sayar da jarirai a Nasarawa

Advertisement

 

A tsakiyar rikicin dai akwai Jimi Lawal da Oladipupo Adebutu, dukkansu ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar PDP wadanda suka yi ikrari da kin amincewa da tikitin takarar.

Advertisement

Lawal wanda ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar PDP a ranar 25 ga watan Mayu, ya kalubalanci fitowar Adebutu, inda ya yi zargin cewa jam’iyyar ta yi amfani da jerin sunayen wakilai da ba bisa ka’ida ba wajen gudanar da zaben.

Daga cikin sauran, Lawal ya yi rokon cewa a soke zaben fidda gwani na ranar 25 ga watan Mayu, sannan a gudanar da wani tare da ingantattun wakilan jam’iyyar.

Advertisement

Sai dai mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya a hukuncin da ya yanke a ranar 29 ga watan Yuli ya ki sauraron karar Lawal bisa hujjar cewa zaben fidda gwani na cikin gida ne na kowace jam’iyyar siyasa, ya kuma yi watsi da karar.

Daga bisani kotun koli a ranar 21 ga watan Nuwamba ta umarci babbar kotun tarayya da ta saurari karar da Lawal ya shigar a kan PDP da Adebutu.

Advertisement

Mai shari’a Ibrahim Saulawa na kotun kolin ya bayar da umarnin a gaggauta sauraron karar bayan da ya ce babbar kotun tarayya na da hurumin sauraren karar.

A zaman da aka yi na ranar, Mai shari’a Ekwo, bisa bin umarnin kotun koli, ya saurari karar cikin gaggawa ganin yadda shari’ar za ta tashi zuwa ranar 2 ga watan Disamba.

Advertisement

Mai shari’a Ekwo ya ce zai yanke hukunci a karar a ranar 1 ga watan Disamba, 2022.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending