Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 7, Sun Sace 5 A Sabon Hari A Sakkwato

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum bakwai tare da yin garkuwa da wasu biyar a wasu sabbin hare-hare a kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

 

Aminiya ta rawaito cewa Maharan sun kashe mutum shida a kauyen Bare, daya kuma a Kagara, suka sace mutum biyar, ciki har da wani magidanci da matansa biyu a kauyen Faji, sannan suka wawushe kaya da ba a san iyakarsu ba a shagunan jama’a.

Advertisement

Ina fargabar sakamakon zaɓen 2023 – Jega

 

Yankunan da aka kai wa harin sun hada da, Bare, Kagara, Kojiyo a Karamar Hukumar Goronyo da kuma kauyen Faji a Karamar Hukumar Sabon Birni.

 

Da yake tabbatar da harin, Shugaban Karamar Hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba wasu mutum biyar da dabbobi a kauyukan.

 

 

Advertisement

A cewarsa, an kai harin ne a ranar Laraba da yamma.

 

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, amma ya ce ba shi da labari, amma ya yi alkawarin samun cikakken bayani.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending