News
Gwamnatin Najeriya na shirin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin ƙasar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin ƙasar.
Babbar kwamishiniya a ma’akatar kula da ‘yan gudun hijira da kuma ‘yan cirani, Imaan Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana hakan a jiya Juma’a yayin raba wa ‘yan gudun hijra guda 100 kayakin yin sana’o’i a wasu sansanoni da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
An yanke wa attajiri Jimmy Lai hukuncin daurin kusan shekaru 6 a gidan yari
Ta ce wadanda aka raba wa kayakin suna samun horo a fannin sana’o’i daban-daban domin samun kwarewa.
Ta ce hakan na cikin wani shiri da gwamnati ke yi na rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin ƙasar domin wadanda rikice-rikice ya ɗaiɗaita su samu damar komawa gidajensu.kamar yanda bbc hausa ta rawaito
Ya zuwa watan Agustan 2022, Najeriya na da sansanonin ‘yan gudun hijira miliyan 3.4, sai dai bayan mummunar ambaliya ta ɗaiɗaita al’ummomi a fadin ƙasar, alkaluman sun ƙaru zuwa miliyan 5.
