Connect with us

News

Yan Tunisiya na zanga-zangar neman shugaba Kais Saied ya sauka daga mulki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka mamaye titin da ke Tunis babban birnin kasar, suna kira da shugaba Kais Saied ya sauka daga mukaminsa.

Advertisement

 

Zanga-zangar na zuwa ne mako guda gabanin zabukan da za su kai yin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin shugaba Saied, wanda ake ganin zai samar da majalisar jeka na yi ka.

Advertisement

An yanke wa attajiri Jimmy Lai hukuncin daurin kusan shekaru 6 a gidan yari

Wakilin BBC ya ce ‘yan adawa na zargin shugaban da kitsa wani abu mai kama da juyin mulki a watan Yulin 2021, inda ya kori manyan jami’an gwamnati ya kuma ruguje majalisar dokokin kasar, kuma tun daga nan yake aiki da dokar soji.

 

Advertisement

Tunisia na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da na tabarbarewar tattalin arziki da gurguncewar siyasa da hauhawar farashin kayayyaki da dai sauransu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending