Connect with us

News

Shugaba Ramaphaso na fatan a sake zabarsa shugabancin ANC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Mambobin jam’iyyar ANC da ke mulki a Afrika ta Kudu na hallara a birnin Johannesburg domin wani taro da shugaba Cyril Ramaphosa ke fatan a sake zabarsa a matsayin shugaban jam’iyyar, duk kuwa da wata badakala a baya-bayan nan.

 

Advertisement

Mista Ramaphosa ya kaucewa binciken tsige shi a farkon makon nan, lokacin da akasarin ‘yan majalisar wakilan jam’iyyarsa suka kada kuri’ar kin amincewa da wani rahoto da ya gano cewa watakila ya karya dokar yaki da cin hanci da rashawa bayan sace wasu makudan kudade a gonarsa.

Yadda Tankar Mai Ta Yi Bindiga Ta Kone Shaguna Da Gidaje

Babban abokin hamayyarsa a neman shugabancin shi ne tsohon ministan lafiya, Zweli Mkhize, wanda shi ma ake zarginsa da cin hanci da rashawa.

Advertisement

 

Wani wakilin BBC a Johannesburg ya ce akwai yiwuwar Mr Ramaphosa zai ci gaba da rike mukaminsa, duk da koma bayan da aka samu a baya-bayan nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending