Connect with us

News

Dole a daina kaiwa kayayyakin INEC hari – Farfesa Mahmoud

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi kira ga jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a kasar, da su yi duk abin da za su yi domin ganin an daina kai wa kayayyakin zaben 2023 hari a ko ina.

 

Advertisement

Ya yi wannan kira ne lokacin da yake tattaunawa da majalisar wakilai da kuma kwamiin da yake bincike kan hare-haren da ake kaiwa kan kayayyakin hukumar.

Za A Haramta TikTok A Ma’aikatun Amurka

Ya ce hukumar ta fuskanci hare-hare 50 cikin jihohi 15 a 2019, Farfesa Yakubu ya bayyana wasu daga cikin jihohin da abun ya faru da suka hada da Imo wadda aka kai hari 11, sai Osun da ke da bakwai, an kai hare-hare biyar a jihar Enugu.

Advertisement

 

Sauran sun hada da Akwa Ibom da ita ma akai kai hari biyar, an kai hare-hare hudu a jihohin Cross River da Abiya.

Advertisement

 

Ya ci gaba da bayyana yadda aka kai hare-hare biyu a jihohin Anambra da Taraba, sai johohin Bayelsa, Ondo, Lagos, Borno, Kaduna da kuma Ogun da dukkansu aka kai musu hari sau daya.

Advertisement

 

Yayin da kwamitin yake tattaunawa kan yadda za a maye gurbin kayyakin da aka lalata, Farfesa Mahmoud ya bayyana cewa zabe ba zai taba yiwuwa ba a haka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending