Connect with us

News

Gwamnatin Kaduna za ta mayar wa mutane baburan su da ta ƙwace

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen-hawa ta Jihar Kaduna, KASTLEA, ta ce za ta saki dukkan baburan da ta kama a shekarar 2022, daga ranar Talata.

 

Advertisement

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashiyar shugaban hukumar KASTELIA, Carla Abdulmalik, ta fitar ranar Lahadi a Kaduna.

Kotu ta yanke wa Doyin Okupe shekaru 2 a gidan yari

Sai dai ta ce dole ne masu baburan da aka kama su biya tara tare da sabunta takardunsu.

Advertisement

 

Mukaddashiyar shugaban hukumar ta ce za a gudanar da atisayen ne a rukuni-rukini daga ranar 20 ga Disamba, 2022 zuwa 20 ga Janairu, 2023.

Advertisement

 

A cewar ta, za a gudanar da aikin tantance takardun ne a filin wasa na Ahmadu Bello, inda za a cike fom da kwafin takardu, tare da sanya hannu na yarjejeniya.

Advertisement

 

Daily Nigerian hausa ta rawaito cewa“ Babura da ba su yi rajista ba za su biya Naira 30,000 kowannensu, sannan wadanda ba su da lamba ko bayanai za su biya N12,000 kowanne.

Advertisement

 

“Masu baburan da suka yi rajista za su biya N20,000 da kuma N3,700 don sabunta bayanai, jimlar N23,700.

Advertisement

 

“Ana sa ran masu babura su gabatar da katin shaidar dan kasa, takardar sayen babur, bayanan rajista da kuma hotunan fasfo, kafin a sako musu baburan,” ta kara da cewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending