News
mutum tara sun mutu a turmutsutsun murnar sabuwar shekara a Ugandan
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Akalla mutum tara ne aka tabbatar da cewa sun mutu a wani turmutsutsun murnar sabuwar shekara a Kampala babban birnin Uganda.
Lamarin ya faru ne a daidai sa’o’in farko na shiga sabuwar shekarar a harabar babban kantin sayar da kayyaki mai suna Freedom City Mall, da ke tsakiyar birnin Kampala.
Aston Villa ta ƙara wa Conte matsin lamba bayan doke Tottenham 2-0
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar Luke Owoyesigyire, ya ce lamarin ya faru ne ”sakamakon yawan mutanen da suka fita domin kallon tartsatsin wuta”.
Ya ce mutum biyar ne suka mutu nan take, yayin da wasu ƙarin hudu suka mutu a asibiti sakamakon munanan raunukan da suka ji.
Advertisements
