A nan gaba kaɗan ne a yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2023, kasafin kuɗi na ƙarshe da zai sanya wa hannu a matsayinsa na shugaban ƙasar.
A ranar juma’ar da ta gabata ne shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ne ya sanar da haka ga manema labarai bayan ganawar sirri da shugaban ƙasar a fadarsa da ke Villa.
Brentford Ta Casa Liverpool A Firimiyar Ingila
A makon da ya gabata ne dai ‘yan majalisar dattawa da na wakilai suka amince da kasafin kuɗin da aka ƙiyasta zai ci naira kusan tiriliyon 22.
‘Yan majalisar sun yi ƙarin naira tiriliyon ɗaya da ɗoriya a kan adadin kuɗin da ɓangaren zartarwa ya tura musu.
`Yan majalisar sun bayyana cewa sun amince da kasafin kuɗin ne bayan sun yi nazarinsa ciki da bai, kana suka zartar da shi, har ma suka yi kari a wuraren da suka ga ya dace kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su damar yi.
