Connect with us

News

Matashi Ya Yi Garkuwa Da Mahaifinsa, Ya Karbi Kudin Fansa N2.5m

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta cafke wani matashi bisa zargin laifin yin garkuwa da mahaifinsa har da karbar kudin fansa na Naira miliyan biyu da rabi.

 

Advertisement

Ajayi Okasanmi, kakakin rundunar, wanda ya bayyana hakan, ya ce an kama wanda ake zargin ne a yankin Unguwar Kambi da ke Ilorin, babban birnin jihar.

An haramta wa gwamnatoci cire tsabar kuɗi daga asusu a Najeriya

sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar ne suka cafke wanda ake zargin ne a yayin da aka bi sawun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Advertisement

 

Okasanmi ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin kamo sauran ababen zargin da suka tsere.

Advertisement

 

 

Advertisement

“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da cewa ya hada baki da wasu mutane biyu don sace mahaifinsa, Bature Naigboho a yankin Igboho/Igbeti na Jihar Oyo kuma ya karbi kudin fansa na Naira miliyan 2.5,” in ji Okasanmi.

 

Advertisement

Ya kara da cewa, za a mika lamarin zuwa ga rundunar ’yan sandan Jihar Oyo wadda huruminta ce kasancewar a can ya aikata laifin.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending