Connect with us

News

Muna buƙatar Buhari ya sa baki kan ƙarin kuɗin makaranta – Kungiyar Dalibai

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya NANS ta buƙaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi ”gaggawar sa baki” game da ƙarin kuɗin makaranta da jami’o’in ƙasar ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin ƙasar”.

 

Advertisement

Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa ”duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari”,

Shekara 1 Da Rasuwar Sheikh Ahmad Bamba

A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu daga cikin jami’o’in ƙasar suka bayyana ƙarin kuɗin makaranta.

Advertisement

 

To sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.

Advertisement

 

Dalilin ya da sa kenan suka rubuta wasika ga shugaba ƙasa, inda suka buƙace shi a matsayinsa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya.

Advertisement

 

Wasu jami’o’in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun nasu.

Advertisement

 

To sai dai ƙungiyar ta ce kundin tarin mulki ya wajabta wa gwamnati samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan ƙasa, don haka dole ta samar da kuɗin gudanar da ɓangaren ilimi.

Advertisement

 

Haka kuma Sakataren na NANS ya ce ”matuƙar ba a soke ƙarin kuɗin makarantar da aka yi ba, to kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na ɗaliban ƙasar ba za su koma makaranta ba, saboda ba za su iya biyan wannan kuɗi ba”.

Advertisement

 

Abin da kuma a cewarsa zai ƙara yawaitar masu aikata miyagun laifuka a fadin ƙasar saboda rashin makoma da ɗaliban ke da shi.

Advertisement

 

Mista Kankia ya kuma yi gargaɗin cewar ”matukar buƙatarmu ba ta biya ba, to za mu gudanar da gagarumar zanga-zangar da za ta shafi abubuwa da dama a faɗin kasar nan”.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending