News
Jami’ar BUK Ta Musanta Kara Kudin Makaranta Ga Dalibai
DAGA HASSAN KHALID HAMZA
Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta musanta labarin dake yawo gari cewa ta kara kudin makaranta ga daliban dake karatu a cikin da wadanda ke son shiga.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun Jami’ar Lamara Garba, in da ya ce labarin ba gaskiya bane.
Ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, wadda aka wallafa a mujallar Jami’ar, ya bukaci iyayen dalibai, da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulan su.
Sanarwar ta kara da cewa jami’ar har yanzu bata gama tsayar da matsaya ba kan, kudin makaranta da ya kamata dalibai su biya a bana.
Yanzu haka dai jami’o’i musamman na gwamnatin tarayya na ci gaba da kara kudin makaranta ga dalibai.
Lamarin da ke haifar da damuwa ga daliban da iyayen su, suna masu neman da a sassauta.
