News
NUJ ta kori Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA daga Kungiyar.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya, NUJ , ta kori hukumar wayar da kan jama’a ta kasa. NOA daga kundin tsarin mulkin kungiyar
Jaridar indaranka cewa Taron wakilai na musamman da aka gudanar a Afficient event centre a Kano, wanda shugaban kungiyar na kasa Chris Isiguzo ya jagoranta, ya dauki wannan matakin, yayin taron duba kundin tsarin mulkin kungiyar nuj.
Wakilan da ke zama sun ba da sanarwar cewa ba za a sake ba ma’aikatan NOA damar zama mamba na NUJ ba.
Za a ba wa wasu zaɓaɓɓun jami’an NOA damar cika wa’adin aikinsu.
Taron na watan Agusta ya kuma zartas da sabuwar dokar da ta haramtawa ma’aikatan ma’aikatun yada labarai da aka yanke wa hukunci kasancewar ba ‘yan jarida ba ne daga yanzu an hana su shiga kungiyar ta NUJ.
Wakilan da suka halarci zaman sun kuma amince cewa kada a sake baiwa jami’an hulda da jama’a na kananan hukumomi matsayin mambobin kungiyar NUJ.
