Connect with us

Sports

Brighton ta fitar da Liverpool daga gasar cin kofin FA

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

 

Kungiyar kwallon kafa ta Brigton ta yi waje da takwararta ta Liverpol daga gasar cin kofin FA , gasa ta biyu mafi girma a Ingila bayan doke ta a wasansu na jiya da kwallae 2 da 1.

 

Advertisement

 

Kaoru Mitoma ne ya zura kwallo a karin lokaci ana daf ta tashi wasa 1 -1 inda ya taimakawa kungiyar zuwa mataki na gaba tare da yin waje da Liverpool mai rike da kambun gasar.

An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano

Tawagar Jurgen Klopp, wadda aka doke su da kwallaye 3 da nema a Seagulls makonni biyu da suka gabata, ita ta jagoranci wasan, da kwallo daya da nema, kwallon da dan wasanta na gaba Harvey Elliott ya zura mata.

 

Sai dai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Brighton ta rama kwallon ta hannun Lewis Dunk a minti na 39, kafin dada bisani ta kara kwallo ta biyu ana gab da tashi.

 

Advertisement

 

Rashin nasarar ko kuma kubcewa kambun na FA da Liverpool ke karewa a kara matsin lamba ga Manaja Jurgen Klopp wanda tuni aka fara kiraye-kirayen korar shi.

 

Liverpool dai na fama da rashin nasara ne a wannan kaka inda ta ke ganin mummunan koma baya a teburin Firmiya.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending