News
‘Yan sanda sun gurfanar da wani mutum a Kotu da laifin ya ƙara aure.
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
A ranar Larabar da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da wani mutum mai suna Edmund Uzoma a gaban wata kotun Majistare da ke Yaba a jihar Legas bisa zarginsa ya ƙara aure.
An gurfanar Uzoma a gaban majistare Adeola Olatunbosun bisa tuhomomi guda uku na ƙara auren mace ta biyu da bayar da bayanan ƙarya a jikin katin shaidar aure. Kamar yadda Jaridar The Punch ta rahoto.
Dan sanda mai shigar da kara, Idowu Osungbure, ya shaida wa kotun cewa Uzoma, yayin da yake da mata, ya sake yin wani aure da wata Sophia Yongxian, a wurin rajistar aure.
Ya lura cewa wanda ake tuhumar ya kuma yi shelar karya cewa shi dalibi ne tun yana aure.
Osungbure ya yi zargin cewa Uzoma ya aikata laifin ne a shekarar 2019, inda ya kara da cewa laifukan ana hukunta su a karkashin sashi na 411 da 115 na dokokin laifuka na jihar Legas da sashe na 370 na kundin laifuffuka Cap. C. 38 Dokokin Tarayya, 2004.
A wani bangare na tuhume-tuhumen ya kara da cewa, “Kai Edmund Uzoma, da ke Lekki Road 15, Golden Gate Apartment, Legas, ko a wani lokaci a shekarar 2019 a Legas, a gundumar Majistare ta Legas, kun hada baki a tsakaninku da aikata laifi; bigamy, da maganar karya da shela.”
Wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Alkalin kotun, Olatunbosun ya amince da bada belinsa a kan kudi N1m tare da wasu mutane biyu da suka tsaya masa.
Ta ce tabbas daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya mallaki dukiya a Legas.
Olatunbosun ya dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga Maris, 2023.
