Connect with us

News

Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan shari’ar Ahmad Lawan da Bashir Machina

Published

on

DAGA ABDULRASHEED MUHAMMAD RABIU 

 

Advertisement

 

A yau ne kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci game da rikicin takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa na jam’iyyar APC.

Advertisement

 

Jam’iyyar APC na ƙalubalantar Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa.

Advertisement

Yan Najeriya Na Bukatar Mako 2 Don Su Murmured Bayan Saukar Buhari  – Kato

Jam’iyyar ta kafe cewa shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ne halastaccen ɗan takararta a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

 

Advertisement

A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam’iyyar Sepiribo Peters ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.

 

Advertisement

Peters ya ce ba jam’iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin ba.

 

Advertisement

Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaɓen fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaɓen.

 

Advertisement

Ya kuma ce kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya sake shirya wani zaɓen fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara.

 

Advertisement

Bbc ta rawaito cewa, To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce yana fatan Kotun Ƙolin za ta yi watsi da ƙarar sakamakon rashin ƙwararan hujjoji, kasancewar Shugaban Majalisar Dattawan bai ƙalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.

 

Advertisement

Ya ƙara da cewa mutumin da ya jagorancin zaɓen da ya bai wa machina nasara mamba ne a kwamitin gudanarwar jam’iyyar, wanda kuma aka naɗa domin ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending