News
Yan Najeriya Na Bukatar Mako 2 Don Su Murmured Bayan Saukar Buhari – Kato
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Daya daga cikin mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Ndi Kato, ya ce ‘yan Najeriya za su bukaci hutun akalla mako biyu don murmurewa daga hannun gwamnatin Shugaba Buhari.
Sanarwar hakan na kunshe ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Asabar.
Idan dai za a iya tunawa dai an yiwa kasar nan Caaa ne sakamakon sake fasalin kudin Naira da babban bankin Najeriya CBN ya sauya.
Wannan dai baya ga matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a fadin kasar nan, inda farashin man fetur ya haura N500 a wasu Jihohin kasar.
Sai dai Kato ta fito ta koka kan yadda ‘yan Najeriya suka sha wahala a wannan zamanin.
Ta rubuta cewa, “Lokacin da Buhari ya sauka daga mulki, muna bukatar hutun makwanni akalla 2 domin mu samu murmurewa.
“Yan Najeriya, hakika mun sha wahala.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
