Connect with us

News

EU ta haramta wa ma’aikatanta amfani da manhajar TikTok a na’urorinta

Published

on

 

Hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai ta faɗa wa ma’aikanta da su cire manjahar TikTok mallakar ƙasar China daga wayoyinsu na aiki da sauran naurori saboda dalilan tsaro.

Advertisement

 

Mai magana da yawun hukumar Sonya Gospodinova ta ce EU ta ɗauki wannan matakin ne domin inganta tsaro a harkar intanet ɗin ta.

Advertisement

Mace 1 Na Mutuwa Duk Minti 2 Wajen Haihuwa —WHO

Gwamnatocin ƙasashen yamma na fargabar cewa China za ta iya amfani da manhajar mai farin jini domin leƙen asiri.

 

Advertisement

A bara ne gwamnatin Amurka ta hana amfani da Tik-Tok ɗin a naurorinta.

 

Advertisement

Sai dai kamfanin Tik-Tok ya ce akwai rashin fahimta a matakin da EU ta ɗauka

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending