News
Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Nasara A Ogun, Atiku A Matsayi Na Biyu
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe zaben shugaban kasa a jihar Ogun, inda ta doke jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun siyasa.
A cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Ogun, dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zo na daya da kuri’u 341,554, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu kuri’u 123,831.
A matsayi na uku, na hudu da na biyar, Peter Obi na Labour Party (LP) ya samu kuri’u 85,829, Dumebi Kachikwu na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da 10,529, sai Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) 2,200.
Adadin masu kada kuri’a a jihar ya kai 2,687,606 inda jimillan wadanda aka amince da su ya kai 612,341.
Adadin kuri’un da aka kada ya kai 611,448, wanda ya kunshi sahihin kuri’u 580,124 da kuri’u 31,324 da aka ki amincewa.
Channel
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
