News
’Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 3, Sun Sace Wasu 16 A Kauyukan Kaduna
Kasa da awa 24 bayan ’yan bindiga sun sace wani jaririn da wata mai jego ta haifa a sansaninsu, an sake kashe mutum uku tare da sace wasu 16 a kauyuka uku na Karamar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna.
Wani mazaunin yankin, Shehu Rabi’u, wanda ya tabbatar wada daily trust a faruwar harin ta wayar salula ranar Laraba, ya kuma ce an kai hare-haren ne a kauyukan Kala da Kutar da kuma Taka-Lafiya.
FIFA ta karbe daukar nauyin gasar kofin duniya daga Indonesia
Ya ce maharan, wadanda ke kan babura dauke da bindigu kirar AK-47, da farko sun kai hari ne kan wani matsugunin makiyaya da ke Taka-Lafiya, inda suka sace mutum shida, sannan suka kashe wani mai suna Malam Ya’u.
Ya ce daga nan ne maharan suka wuce kauyen Kutar mai makwabtaka da shi, inda a can ma suka yi awon gaba da mutum bakwai.
Kazalika, Shehu ya ce ’yan bindigar sun kuma karasa kauyen Kala suka sace mutum biyar bayan sun yi ta harbe-harbe.
“A lokacin da suke ta harbe-harben ne mutum biyu suka mutu a Taka-Lafiya, daya kuma a Kutar,” in ji Shehu.
Shi ma Madakin Janjala, wani kauye da ke da makwabtaka da inda aka kai hare-haren, Sama’ila Babangida, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa Jere lokacin da ya samu labarin.
Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar dai na da sansanoninsu a Tagwayen Dutse, wani dajin gwamnati da ke tsakanin Kananan Hukumomin Kagarko da Kachia na jihar Kaduna.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wani karin bayani kan batun daga Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kadunan.
-
News7 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News7 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
