Connect with us

News

Mata kusan 30 na mutuwa sanadin kansar bakin mahaifa a Najeriya

Published

on

Cibiyar bincike kan ayyukan likitanci a Najeriya ta ce duk da matakan rigakafin da ake ɗauka, mata 28 na mutuwa duk rana sanadin cutar kansar mahaifa a ƙasar.

Cibiyar ta yi magana kan buƙatar yi wa ƴan mata rigakafi da kuma tantance mata domin cike giɓin da ake da shi.

Advertisement

’Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’a Mata Biyu A Zamfara

Da yake magana a wani taro don yin ƙarin haske kan ƙaruwar annobar a tsakanin ƴan mata da mata, Daraktan cibiyar, Farfesa Oliver Ezechi, ya yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da su riƙa ɗaukar al’amuran da suka shafi lafiyar mata da muhimmanci.

Da yake jaddada cewa ana iya kare samuwar cutar, Farfesa Ezechi ya bayyana cewa kansar bakin mahaifa ita ce nau’in kansar da ta fi ƙamari a tsakanin mata.

Advertisement

Ya ce “duk shekara, ana gano mata kimanin mata 12,000 a Najeriya ɗauke da cutar kuma kusan 8,000 na mutuwa sanadiyyarta. A kowacce rana, kimanin mata 28 ne ke mutuwa sakamakon kansar mahaifa.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending