Connect with us

News

Kuɗin masaukai ya yi tashin gwauron zabo a Makkah

Published

on

 

 

 

Advertisement

An samu ƙarin farashin ɗakunan otal-otal da ke Makkah a watan Ramadan na bana.

 

Advertisement

Wannan Shi ne farashi mafi tsada cikin shekara uku, inda ya kai kashi 80 cikin 100 kamar yadda yake a ƙididdigar da hukumar kula da aikin hajj da umrah ta Makkah ta fitar.

Mata kusan 30 na mutuwa sanadin kansar bakin mahaifa a Najeriya

Farashin otal ɗin a azumin bana ya ƙaru saboda yawan buƙata musamman a cikin kwana 10 na ƙarshen watan.

Advertisement

 

Wani nazari da Al-Eqtisadiah business daily ta yi game da karɓar otal a tsakiyar birnin Makkah cikin goman ƙarshe na Ramadana, farashin ya kai tsakanin SR3,000 zuwa SR9,000 a kullum, idan dakin otal ɗin za a yi amfani da shi ne a cikin goman ƙarshe.

Advertisement

 

Shugaban hukumar, Abdullah Al-Qadi ya ce farashin ɗakunan otal ɗin ya ta’allaƙa ne a kan wasu batutuwa, da kuma ƙarin buƙata da kasancewar kusancin wajen da masallacin Harami.

Advertisement

 

Ya ce abin da ya bambanta farashin ɗakunan otal ɗin a Makkah shi ne kasancewar ɗakunan suna tsakiyar birnin Makkah inda farashinsu kan tashi idan azumi ya gabato, sannan kuma su ninka a goman ƙarshe na watan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending