News
INEC za ta bai wa Fintiri shaidar cin zaɓensa yau La
Hukumar zaɓe mai zamab kanta ta kasa INEC ta ce a yau Laraba ne za ta bai wa gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da mataimakiyarsa farfesa Kaletapwa Farauta shaidar sake cin zaɓe karo na biyu.
Hukumar din ta ce za ta bai wa Fintiri da mataimakiyarsa shaidar cin zaɓen ne da misalin karfe 3 na rana.
A jiya Talata ne jami’in sanar da sakamakon zaɓen jihar Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen da ƙuri’a, 430, 861.
Fintiri ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri’a, 398, 788.
Hukumar ɗin za kuma ta bai wa ƴan majalisar tarayya da na jihohi da aka zaɓa shaidarsu ta cin zaɓe.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
