Connect with us

News

Bashin Da Bankin Duniya Ke Bin Najeriya Ya Kai Tiriliyan 6

Published

on

 

 

Advertisement

Adadin kudaden da Najeriya ta ciyo bashin su daga bankin duniya ya kai naira triliyan 6, abin da ke nufin adadin ya karu da kaso 121.46, karkashin gwamnatin shugaba Buhari.

 

Advertisement

Wata mujalla da ke bincike kan kasashen da babban bankin ke bi bashi ta Economic Confidential ce ta bayyana hakan, ta cikin wani kundi da ta fitar, inda ta ce adadin kudin da gwamnatin Buhari ta ciwo bashin su cikin shekaru 7, sun kai dala biliyan 7 da miliyan 64.

Yau Za A Kwaso ’Yan Najeriya Da Suka Makale A Yakin Sudan

Baya ga wannan kuma, adadin kudaden da Amurka ke bin Najeriyar bashi ya kai dala biliyan 6 da miliyan 24, wato kusan Naira triliyan 2 da miliyan 900 kenan idan aka yi amfani da farashin gwamnati wurin lissafin dalar zuwa naira.

Advertisement

 

Bayanai sun ce kasashen da biyar da bankin ya fi bin bashi sun dan rage yawan kudaden da ake binsu amma banda Najeriya.

Advertisement

 

Tuni dai masana tattalin arziki suka fara hasashen cewa gwamnati mai zuwa a kasar na iya fuskantar kalubalen biyan basussukan da ake bin Najeriya idan ba a dauki matakin da ya dace wurin rage yawan cin bashin da ake yi yayin da kasar ke fama da karancin kudin shiga.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending