Connect with us

News

Amurka ta haramta wa ‘yan Najeriyan ‘da suka yi laifukan zaɓe’ shiga ƙasar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ɗauki matakin haramta wa wasu ‘yan Najeriya shiga ƙasarta, waɗanda ta ce sun taka rawa wajen kassara dimokradiyyar ƙasar a lokacin zaɓukan ƙasar na 2023 da suka gabata

Advertisement

A wata sanarwar da ofishin jakadancin ya fitar ya ce ya ɗauki matakin ne domin ƙarfafa tare da nuna goyon bayansa ga tsarin dimokradiyyar ƙasar da ma duniya baki-daya.

Akwai fargabar karatun daliban da dama a Jami’ar Yusuf Maitama Sule ya zai iya tsaya – Shugabar Dalibai

Sanarwar ta ce ”Mun ɗauki matakin ƙaƙaba haramcin bayar da biza ga wasu mutane a Najeriya da suka taka rawa wajen yi wa dimokradiyyar ƙasar zagon-ƙasa musamman a lokacin zaɓukan 2023”

Advertisement

Sanarwar ta ci gaba da cewa an ɗauki matakin ne kan wasu tsirarun mutane, ba wai al’ummar ƙasar ko gwamnati ba.

”A ƙarƙashin dokokin ƙasarmu, waɗannan mutanen ba su cancanci samun biza zuwa Amurka ba, sakamakon rawar da suka taka wajen yi wa dimokradiyyar Najeriya zagon ƙasa”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Advertisement

Sanarwar ta ce mutanen sun aikata laifukan da suka ƙunshi razanar da masu kaɗa ƙuri’a ta hanyar yi musu barazana, da tayar da hargitsi, da sauya sakamakon zaɓe da sauran laifukan da suke yi wa dimokradiyyar ƙasar zagon-ƙasa.

Matakin kamar yadda sanarwar ta yi bayani na zuwa ne don nuna goyon bayan da Amurka ke bai wa Najeriya wajen ƙarfafa tsarin dimokradiyyarta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending