News
An Kai Hari Kan Kwambar Motocin Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Fadar gwamnatin Amurka ta tabbatar da kai hari kan ayarin motocin ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, to amma ta ce babu ɗan ƙasarta ko ɗaya da harin ya shafa.
Lamarin ya auku ne ranar Talata a ƙaramar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar nan.
Majalisa Ta 10: Tsarin Karba-karba Na Jam’iyyar APC Bai Ma Arewa Adalci Ba
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka, John Kirby na cewa ”babu Ba’amurke ko ɗaya da harin ya ritsa da shi”..
To sai dai Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe wani ma’aikacin ofishin jakadancin a yayin harin da aka kai wa kwambar motocin.
Ta ambato wata majiya na shaida mata cewa an kashe a ƙalla mutum huɗu, yayin da wasu suka jikkata a harin.
Shi ma Mista Kirby ya ce sun samu rahoton rasuwa da jikkata, sai dai ya ce ba zai yi ƙarin bayani ba.
