Connect with us

News

Gwamna Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartaswa Mako Ɗaya Gabanin Mika Mulki  

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Gwamnan Kano mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sallami baki ɗaya mambobin majalisar zartarwa daga bakin aiki.

Ganduje ya rushe majalisar zartaswansa a wani ɓangare na shirye-shiryen miƙa mulki ga zababben gwamna ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Advertisement

Babbar Sakatariya a ofishin Sakataren gwamnatin jihar Kano, Bilkisu Maimota, ce ta bayyana haka a wata sanarwa a ranar Litinin.

Zargin Kisa: Kotu Ta Hana Kara Daukar Mataki A Kan Doguwa

Sanarwar ta ce “Yayin da wa’adin zango na biyu na mulkin Gwamna Abdullahi Ganduje zai cika ranar 29 ga watan Mayu, 2023, ya zama wajibi jami’an gwamnati da ke riƙe da kujerun siyasa su sauka daga mukamansu.”

Advertisement

 

“Bisa haka ne, a hukumance muke umartan masu rike da naɗe-naɗen siyasa kama daga Kwamishinoni, mashawarta da sauran hadimai na musamman, mambobin gudanarwan hukumomi su miƙa ragamar ofisoshinsu.”

Advertisement

“Dukkan waɗanda abun ya shafa ana umartar da su miƙa ragama da duk wata kadarar gwamnati hannun Manyan Sakatarori ko Daraktoci daga nan zuwa ranar Jumu’a 26 ga watan Mayu.”

“Bugu da ƙari, Bilkisu Maimota, ta ce wannan umarnin bai shafi masu rike da muƙaman da wa’adinsu bai ƙare ba kamar yadda kundin dokoki hukumomin su suka ya tanada.

Advertisement

Ta bayyana cewa Gwamna Ganduje ya gode tare da jinjinawa jami’an gwamnatin bisa gudummuwar da suka bayar iya karfinsu wajen kawo ci gaba ga jahar Kano.”

Mai girma Gwamna ya na musu fatan Alheri a dukkan harkokin rayuwar da zasu sa gaba, inji Maimota.

Advertisement

 

Wa’adin Gwamna Ganduje zai ƙare a Litinin mai zuwa wato 29 ga watan Mayu, inda za a rantsar da Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin sabon gwamnan jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending