Connect with us

News

Sama Da Tan 400 Na Shara Muka Kwashe A Sassan Jihar Kano – Aliyu Yakubu Garo

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Kwamitin hadin karta kwana kan aikin kwashe shara a cikin birnin Kano ya yi nasarar kwashe fiye da Tifa dari hudu cikin sa’o’i 72.

Babban sakataren ma’aikatar muhalli ta jihar Kano Alhaji Aliyu Yakubu Garo shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ziyarar dubawa da kuma sa ido kan yadda ake kwashe sharar a cikin kwaryar birni.

Advertisement

Hukumar NAHCON Ta Nanata Dokar Mahukuntan Kasar Saudiyya Kan Shiga RAUDAH

Wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Ismail Garba Gwammaja ya sanyawa hannu, ta ce babban sakataren wanda ya ziyarci wurare kusan 20 a cikin birnin Kano ya bukaci mazauna jihar da su tallafawa kokarin gwamnati na ceto muhalli daga hatsarin sauyin yanayi.

A cewarsa, gwamnati mai ci ta nuna sha’awarta da kuma himma wajen kare rayuka ta hanyar inganta tsaftar muhalli da kuma kudirin wajabta sanya kwando ga direban mota da sauran sabbin tsare-tsare.

Advertisement

 

arewa radio

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending