News
An kama wanda ake zargi da fashi da makami bayan kwana 3 da barin gidan yari
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An sake kama wani da ake zargin dan fashin ababen hawa ne mai suna Kingsley kwanaki uku bayan an sako shi daga cibiyar gyaran hali ta Ikoyi.
Mutumin mai shekaru 45 da haifuwa an kama shi ne tare da wasu 6 yayin da ake zarginsa da yin fashin ga wasubmatafiya da aka tsare a cikin cunkoson ababen hawa a unguwar Ijora Badia da ke Legas.
An kama wani ma’aikacin jinya da wasu ma’aikata biyu bisa bacewar mahaifa a cikin asibitin
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya kulla alaka ne da ‘yan kungiyarsa na baya a yankin farin yashi na Ijora-Badia bayan an sako shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar wa manema labarai kamun a ranar Talata, ya ce wadanda ake zargin sun yi wa fasinjoji fashi ne a cikin ababen hawa a lokacin da aka yi tashin gwauron zabi a ranar Asabar.
Ya ce rundunar ‘yan sanda ta Ijora Badia ta gudanar da wannan aika-aika ne a cikin sa’o’i masu tsanani na zirga-zirga a wurare daban-daban a Ijora/Apapa a ranar Asabar da misalin karfe 9:30 na dare.
Ya ci gaba da cewa, “Sakamakon hadin gwiwa da kungiyoyin ‘yan sintiri na rundunar ‘yan sanda ta Ijora Badia suka yi, ya kai ga cafke wadanda ake zargin a wurare daban-daban a kan gadar Total, daura da yankin Apapa, da Ijora Badia.
Daily trust ta rawaito cewa “Daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Kingsley (43) an sake shi daga gidan gyaran hali na Ikoyi kwanaki uku kafin kama shi. Sauran wadanda ake zargin ‘yan shekara 19 zuwa 25 ne, ana zarginsu da yin fashin motoci ne.”
Wanda ya yi hoton ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
