Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton ƙungiyar Tarayyar Turai kan zaɓen 2023

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) game da sakamakon babban zaɓen 2023 da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban ƙasar.

Cikin rahoton nata, ƙungiyar ta ce sunan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa  INEC ta ɓaci, musamman saboda gazawa wajen ɗora sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a shafin intanet a lokacin da ta yi alƙawari tun da farko.

Advertisement

wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shahararren dan kasuwa a jahar  Imo

Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana rahoton a matsayin “maras kan-gado da aka haɗa shi ta hanyar dogaro da abubuwan da suka faru a rumfunan zaɓe ƙasa da 1,000 cikin 176,000 da aka kaɗa ƙuri’a” a ranar zaɓen na watan Fabrairu.

 

Advertisement

“Babban zaɓe na 2023, musamman na shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya lashe, shi ne mafi inganci da zaman lafiya da aka taɓa yi a Najeriya tun shekarar 1999,” in ji Dele Alake, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan ayyuka na musamman.

Kazalika, ya ce babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da EU ko wata ƙungiyar ƙasar waje ta gabatar da za ta yi fatali da ingancin zaɓen na watan Fabrairu, yana mai cewa sauran ƙungiyoyi kamar na rainon Ingila, Commonwealth, da Ecowas, da NBA sun yabi adalci da yadda aka gudanar da shi.

Advertisement

Sai dai har yanzu jam’iyyun adawa na PDP da Labour na ci gaba da ƙalubalantar sakamakonsa a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending