News
Nijeriya ta shirya ƙarfafa ƙawance da ungiyar Ƙasashen Turai don yaƙi da matsalolin tsaro
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ministan Tsaro Mohammed Badaru, ya bayyana cewa a shirye Nijeriya take ta ƙarfafa ƙawance da Ƙungiyar Ƙasashen Turai (EU) a fannin tsaro.
Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar a ofishinsa da ke Abuja.
Kotun Sojoji A Najeriya Ta Kama Babban Soja Da Laifin Satar Fiye Da Biliyan Daya
Ya ce “Nijeriya na so ta farfaɗo da ƙawancenta da EU da ƙarfafa dangantaka wajen yaƙi da matsalolin tsaro.
Ya ce lallai Nijeriya na da buƙatar samun kayayyakin aikin tsaro daga ƙungiyar EU don yaƙi da ƙalubalen tsaro a ƙasar.
A cewarsa, “Manyan matsalolin tsaron da Nijeriya ke fuskanta su ne fashin fadaji a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sai matsalar Boko Haram a Arewa maso Gabas da satar mai a Kudu maso Kudu, da kuma matsalar masu neman ɓallewa a Kudu maso Gabas da matsalar tsaro a yankin tabkin Chadi.”
Jagorar tawagar kuma Mataimakiyar Babban Sakataren EEAS, Helena Konig, ta ce sun yi ziyarar ne domin sanin inda EU za ta shigo don tallafa wa Nijeriya a ɓangaren tsaro.
A wani labarin kuma Kotun Sojoji A Najeriya Ta Kama Babban Soja Da Laifin Satar Fiye Da Biliyan Daya
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
