Connect with us

News

Kotun Sojoji A Najeriya Ta Kama Babban Soja Da Laifin Satar Fiye Da Biliyan Daya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Kotun Sojin Najeriya ta musamman da ke zamanta a Abuja ta ce ta samu Maj-Gen Umaru Muhammed da laifin satar $1.476m.

Muhammed shi ne tsohon shugaban kungiyar Nigerian Army Properties Limited, NAPL.

Advertisement

An Kori Karen Joe Biden Daga fadar gwamnatin kasar ta White House Saboda Yawan Cizon Mutane

Shugaban kotun, Maj.-Gen. James Myam, ya ce a ranar Larabar da ta gabata, a yayin da ake shari’ar, wanda ake tuhumar ya ki amsa laifinsa, inda ya gabatar da shaidu biyu.

Ya ce kotun ta samu wanda ake kara da laifin satar dalar Amurka miliyan 1.04 tsakanin 7 ga Mayu, 2019, zuwa 24 ga watan Yuni, 2021, a lokacin da yake aiki a matsayin GMD na NAPL.

Advertisement

Shugaban kotun ya kara da cewa, an samu wadanda ake tuhumar da laifin umurtar wani Manjo Usman da ya ajiye kudaden a asusun banki.

Mista Myam, ya ce ba a sami Mista Muhammed da laifi ba a shari’a ta 7, wanda ke da iyaka da hada baki da laifuka na jabun takarda tare da wani Yusuf Abdulahi.

Advertisement

Sai dai an same shi da laifin yin karya dangane da tuhume-tuhume 8 da 9 na satar dala 430,800, in ji shugaban kotun.

Kotun ta kuma samu Janar din da laifin hada baki wajen hada takardu, da kuma sayar da kadarorin kamfanin a lokacin da ya daina aiki a NAPL kan Naira miliyan 200.

Advertisement

Ta kuma same shi da laifin rashin gaskiya da karbar Naira miliyan 74 daga asusun kamfanin a ranar 22 ga Agusta, 2019.

A wani labarin kuma An Kori Karen Joe Biden Daga fadar gwamnatin kasar ta White House Saboda Yawan Cizon Mutane

Advertisement

Dalilin Da Yasa Muka Amince Da Balarabe Duk Da Cewar Ya Fadi A Lokacin Tantancewa-Majalisa

 

Advertisement

A kan tuhume-tuhume 14, 15, 16, da 18, wadanda ke da alaka da karkatar da kudade da sauran laifuka, kotun ta ce wadanda ake tuhumar ba za su iya bayarda lissafin Naira biliyan 2.5 na kamfanin ba.

 

Advertisement

A shari’a 17, inda ake tuhumar Janar din da fitar da Naira miliyan 750 daga asusun kamfanin, kotun ta ce masu gabatar da kara sun gaza tabbatar da zargin nasu ba tare da wata shakka ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending